‘Yancin Rayuwa Ghana
Kundin Tsarin Mulkin Ghana
Hoto: Office Holidays
Gabatarwa
Matashiya:
Dukkan abin da za a karanta daga wannan gaɓa zuwa ƙarshen wannan shafi, fassara ce kai tsaye daga Kundin Tsarin Mulkin Ghana na shekarar 1996 wanda aka ɗauke a shekarar 2021 daga shafin: https://constitutionnet.org
Sashe na 13: Kariya ga ‘Yancin Rayuwa
Wannan sashe ya zayyana waɗannan tanade-tanade a matsayin 'yancin duk wani ɗan Ƙasar Ghana ta fuskacin rayuwa.
- Babu wani mutum da za a raba shi da ransa haka kurum saidai a yanayi na zartar da hukuncin kotu cikin abin da ya shafi manyan laifuffuka a ƙarƙashin dokokin Ƙasar Ghana wanda aka yanke masa hukunci.
- Mutum ba za a tuhume shi da laifin hana wani rayuwarsa ba bisa tanadi na (1) na wannan sashe idan har wancan mutumin ya mutu a sakamakon halastaccen yaƙi ko kuma wancan ɗaya mutumin ya mutu a sakamakon amfani da ƙarfi bisa gwargwadon yadda za a iya tabbatar da gaskiyar hakan a takamaiman yanayi:
- bisa dalilin kare kowane mutum ne daga ruɗanin-rikici ko a dalilin kare dukiya; ko
- domin a aiwatar da halastacciyar tsarewa ko a hana kuɓucewar mutumin da ake tsare da shi bisa doka; ko
- bisa dalilan kwantar da tarzoma, bore ko tawaye; ko bisa yunƙurin kare hukumar kula da laifuffuka (commission of crime) daga wannan mutumin.